Aliko Dangote |
Attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya bada gudummawar Naira Miliyan 150 domin taimakawa wajen yaki da yaduwar cutar Ebola a Najeriya.
Shugaban gidauniyar Dangote Mrs Ahiambo Odaga ta bada sanarwar a wani zama da akayi da Ministan Lafiya a babban birnin tarayya Abuja.
Madam Odaga ta bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi kira ga ' yan Najeriya da su bada goyon baya ga Gwamnatin Tarayya wajen yaki da cutar Ebola inda ya bayyana fatansa na magance Cutar.
No comments:
Post a Comment