Friday, August 15, 2014

Likitoci masu neman kwarewa sun yi zanga-zanga


Likitoci masu neman kwarewa sun yi zanga-zanga domin nuna rashin gamsuwarsu bisa matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na korar likitoci kusan dubu goma sha shida a kasarnan.

Likitocin wadanda suka gudanar da zanga-zanga akarkashin kungiyarsu, sun bayyana takaicinsu ga uwar kungiyar likitoci ta kasa a birnin Abuja.

Shugaban kungiyar likitocin masu neman kwarewa Jibril Abdullahi ya yi Allah wadai da matakin da gwamnatin ta dauka na soke koyarda aikin kwarewa akanaikin likita akasarnan.

Da yake karfafa musu gwiwa shugaban kungiyar likitoci ta kasa(NMA)Dr. Kayode Obembe ya bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta janye kalamanta nadakatar da likitocin.

Masu zanga-zangar daisuna dauke da kwalaye dauke da kalamai daban-daban

Dangote ya bada gudummawar Naira Miliyan 150 domin yaki da cutar Ebola


Aliko Dangote

Attajirin nan Alhaji Aliko Dangote ya bada gudummawar Naira Miliyan 150 domin taimakawa wajen yaki da yaduwar cutar Ebola a Najeriya.

Shugaban gidauniyar Dangote Mrs Ahiambo Odaga ta bada sanarwar a wani zama da akayi da Ministan Lafiya a babban birnin tarayya Abuja.

Madam Odaga ta bayyana cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi kira ga ' yan Najeriya da su bada goyon baya  ga  Gwamnatin Tarayya wajen yaki da cutar Ebola inda ya bayyana fatansa na magance Cutar.

Gwamnan Katsina ya auri 'yar Umaru Musa 'Yaradua





        Gwamna Ibrahim Shehu Shema da Amaryarsa Maryam Umaru 'Yaradua

A yau juma'a 15 ga watan Agusta ne  gwamnan jihar Katsina Barista Ibrahim Shehu Shema zai angwance da amaryarsa Maryam 'Yaradua, 'yar fari ga tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa 'Yaradua.

Za a daura auren ne a sabon masallacin Usmanu Dan Fodio dake birnin na Katsina.

Idan za a iya tunawa Maryam ta taba auren dan sarki Kabir, Badamasi Usman Kabir wanda Allah ya yiwa rasuwa.

Haka kuma kanwarta Nafisa maidaki ce ga  gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda.

Muna taya su murna Allah ya bada zaman lafia, Amin.

Shafin Hatsin Bara ya dawo...

Assalamu alaikum makaranta wannan shafi, ya aka ji da hakuri da mu?.Dafatan anyi azumi lafia kuma anyi bikin sallah karama lafia...Allah ya karbi ibadunmu ya maimaita mana muga na badin ba-da-da lafia.

Wannan shafi na Hatsin bara zai fara da neman afuwarku makaranta...saboda shiru na dan wani lokaci...Amma ina tabbatar muku cewa ya dawo bakin aiki...sai a kasance da shafin.