Ayayin da ake rantsar da sanata Bukola Saraki |
Zaman Majalisar na Yau da Akawun Majalisar Salisu Maikasuwa ya Jagoranta ya samu halartar Sanatoci 57.
Saraki dake wakiltar Kwara ta tsakiya ya zamo shugaban majalisar dattawa bayan sanata Ahmad Yarima Da Deno Milaye suka gabatar da sunansa amatsayin dan Takara.
Yayin da a hannu guda,Ike Ekweremadu ya sake darewa akan mukaminsada ya rike a majalisa ta 7 amatsayin mataimakin shugaban majalisa.
Ekweremadu ya yi Nasarar kayar da abokin takararsa Sanata Ali Ndume.