Sunday, March 16, 2014

A tare mu a shirin Lafiyar Iyali na yau...


Ina Iyaye mata?, yau filin Lafiyar Iyali zai tattauna akan Shayarwa wato Breastfeeding,dan haka a tare mu da karfe 3.30 na yamma domin jin shirin a tashar mu ta wazobia akan Mita 95.1 ko a sauraremu ta www.wazobiafm .com(Kano)

Yau Baide din Jarumi Ali Nuhu...




Jarumi Ali Nuhu




A yau ne 16 ga watan Maris,Shahararren dan wasan Kannywood da Nollywood wand har yanzu tauraruwarsa ke ci gaba da haskawa, Ali Nuhu ya kara shekara daya akan shekarunsa.

        Muna taya shi fatan alheri,Allah kuma ya karo shekaru masu albarka!!

Monday, March 10, 2014

Jaruma Zainab Idris ta zama amarya!!


Amarya Zainab Idris
A Jiya Lahadi ne jarumar kannywood Zainab Idris ta zama amarya  tare da angwanta........An dai daura auren ne a masallacin dake Unguwar Shagari Kwatas, daga bisani aka rakashe a Dakin taro na Darul Tauhid cikin Kano.

Kafin auren ta, jarumar Kannywood ce,daga cikin fina-finanta akwai Hafsah, Kallabi, Guda,Sual, Gwamnati, .Da Sauransu da bisani ta zama Wakiliyar Kamfanin Sadarwa na Vmobile, Ta koma Kamfanin MTN , in da take gabatar da shirin Dandalin Tashi Mu Tallafeka.

Ga kuma hotunan biki domin kashe kwarkwar idanunku....
                                              Allah ya bada zaman Lafia Amin!!!

Sunday, March 2, 2014

A tare mu a shirin lafiar iyali ...



Mace mai juna biyu
Ina masu sauraron tashar wazobiya akan mita 95.1 musamman mata da mazajensu, yau filin ku ya tabo dan haka a tare mu yau da misalin karfe 3.30 domin jin shirin....A yi sauraro lafia!!!